Aung San Suu Kyi ta yi jawabi kan kyautar Nobel

Aung San Suu Kyi
Image caption Aung San Suu Kyi

Mai fafutukar kare dimokradiyyar nan ta kasar Burma Aung San Suu kyi a karshe ta gabatar da jawabinta na karbar kyuatar Nobel ta zaman lafiya shekaru ashirin da daya bayan ba ta kyautar. Ms Suu Kyi ta ce ba ta kyautar alama ce dake nuna cewa ana sane da irin gwagwarmayar da masu fafutukar kafa dimokradiya da kuma kare hakkin jama'a a Burma da sauran kasashen duniya suke yi.

A lokacin laccar da ta gabatar ta ce kyautar Nobel da aka ba ta ta zaman lafiya shekaru ashirin da daya da suka wuce ta kara bude idanunta ta rika jin cewa duniya ta san da zamanta a lokacin da aka mayar da ita saniyar ware a kasarta.

Aun San Suu Kyi ta kuma bayyana sauye sauyen da ake bullo da su a Burma yanzu da cewa abubuwa ne masu kyau, amma tana mai gargadin da a rika sa ido.

Haka nan ta yi kira da sako dukkan fursunonin siyasa ba tre da gicciya wasu sharudda ba, ta ce koda ma a ce mutum daya ne ake tsare da shi saboda wasu manufofi nasa na siyasa, abu ne da zai kasance mai tayar da hankali.

Aung San Suu Kyi ta je kasar Norway ne a ziyararta ta farko a nahiyar Turai cikin shekaru ashirin da ta yi hukumomin sojan kasar Burma na ma ta daurin talala.

A lokacin da yake bude bikin ba Aung San Suu Kyi kyautar ta Nobel, shugaban kwamitin kyautar Nobel ta Norway, Thorbjorn Jagland ya bayyana ta a matsayin wata muhimmiyar kyauta ga duniya.

Ya ce ta nuna juriya da jajircewa da tsayawa kan manufofinta, duk da irin matakan da hukumomin sojar kasar Burma suka rika dauka na takura ma ta.

Karin bayani