'Majalisar sojin Masar ba ta da hurumin rusa Majalisar Dokoki'

majalisar dokokin Masar Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption majalisar dokokin Masar

Babbar kungiyar siyasar Masar ta 'yan uwa Musulmi ta zargi majalisar mulkin soji da ketare iyakar ikonta bayan da ta rusa majalisar dokokin kasar.

Kungiyar tace sanarwar da majalisar ta bayar ranar Asabar ta rusa majalisar dokokin ba ta kan ka'ida domin a cewarta, sojojin ba su da hurumin bayar da wannan umarni.

Rusa majalisar dokokin dai ya biyo bayan hukuncin da babbar kotun Masar ta yanke ne cewa zaben majalisar dokokin ya sabawa doka kuma ya kamata a sake shi.

Wani kusa a majalisar dokokin ya shaida wa BBC cewa ya samu wasika daga majalisar mulkin sojan dake sanar da shi game da rusa majalisar.

An rusa majalisar dokokin ce yayin da al'umar kasar ta ke zaben shugaban kasa .

Ana fafatawa ne tsakanin tsohon Firayim Minista a zamanin shugaba Mubarak, Ahmed Shafiq, da Muhammed Morsi na kungiyar 'yan uwa musulmi.

Rahotanni daga Masar na nuna cewa jama'a ba su fito sosai ba a ranar farko ta zaben.

Ana danganta hakan da matsayin da galibin matasa suka dauka cewa babu na zabe tsakanin 'yan takarar biyu.

Matasan ne suka kasance gaba gaba a lokacin boren da yayi sandiyar kifar da gwamnatin Hosni Mubarak.

Karin bayani