Ana zaben majalisar dokoki a Girka

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Wani ma'aikacin Hukumar Zabe a Girka

A ranar Lahadi ne 'yan kasar Girka ke kada kuri'unsu a zaben 'yan majalisar dokokin kasar wanda shi ne karo na biyu a cikin makonni shida, bayan zaben da aka gudanar a baya ya gaza samar da gwamnatin da za ta jagoranci kasar.

Wannan zaben dai ka iya zama wata kuri'ar raba-gardama tsakanin masu son kasar ta ci gaba da kasancewa a cikin kungiyar kasashen da ke amfani da kudin Euro da ma wadanda ke son ta fice daga kungiyar.

Jam'iyyun da ke gaba-gaba a zaben sune jam'iyar New Democracy, da Syriza Party, wadanda ke da ra'ayin sauya fasalin yarjejeniyar da aka amince da ita game da tallafin ceto tattalin arzikin da kungiyar ta ba kasar.

'Yan kasar dai sun yi Alla-wadai da tsohuwar gwamnati, bayan ta amince da sharuddan kungiyar kasashen da ke amfani da Euro na tsuke bakin-aljihu, lamarin da ya sanya jam'iyar da ke mulki a wancan lokacin ta gaza yin katabus a zaben da aka gudanar a watan jiya.

Mabambantan ra'ayoyi

Shugabar gwamnatin Jamus, Angela Merkel, wadda ke gaba-gaba a goyon bayan bai wa Girka karin bashi, ta yi kira ga 'yan kasar da su zabi gwamnatin da za ta cigaba da aiwatar da yarjejeniyar tsuke-bakin-aljihu.

Sai dai 'yan kasar na da mabambantan ra'ayoyi game da zaben.

Wasu na ganin cewa zaben ba zai sauya halin matsin da suke ciki ba, yayin da wasu ke cewa suna fatan jam'iyar da za ta yi nasara ta samar da ayyukan yi da inganta rayuwarsu.