An kafa dokar hana fita a Kaduna bayan hare hare

hare hare a Nijeriya Hakkin mallakar hoto s
Image caption hare hare a Nijeriya

Hukumomi a jihar Kaduna dake arewacin Nijeriya sun kafa dokar hana fita, ba dare ba rana, bayan wasu hare haren bam da aka kai a wasu coci coci .

Rahotanni na cewa fiye da mutane ashirin ne suka mutu lokacin da bama baman suka tashi a wasu coci coci a Kaduna da kuma Zaria.

An Ambaci wasu jami'an agaji na cewa wadanda aka jikkata sun haura dari.

'Yan sanda da sauran jami'an tsaro na kokarin dawo da doka da oda.

Wadannan hare hare , wadanda suka haddasa asarar rayuka da jikata jama'a sun kuma tunzura wasu matasa mabiya addinin Kirista, a Kaduna wadanda suka datse hanyar Kaduna zuwa Abuja suka rika kai hari a kan musulmi a matsayin ramuwar gayya.

Wani dan jarida ya ce ya ga gawarwakin mutane goma da aka kwasa zuwa mutuware, bayan da wasu matasa suka far masu a kusa da Gonin Gora.

Wasu kungiyoyi da suka hada da ACF ta dattawan Arewa, da Jama'atu Nasril Islam, da kuma kungiyar 'yan asalin kudancin Kaduna, duk sun la'anci hare haren, suna masu kira ga jama'a da su kai zuciya nesa.

Karin bayani