Hukumar gasar Olympics na gudanar da bincike

Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Filin da za a buga gasar Olympics

Hukumar shirya gasar Olympics ta fara binciken wani zargin da ake yi wa jami'an wadansu kasashe na sayar da tikitin gasar da za a gudanar a birnin London a kasuwannin bayan fage.

Binciken na zuwa ne bayan jaridar Sunday Times ta wallafa labari a kan yadda jami'an hukumar ke sayar da dubban tikitin wasan bisa farashin da ya zarta ka'ida har sau goma.

Jaridar ta yi ikirarin cewa binciken na ta, wanda ta kwashe watanni biyu tana gudanarwa, ya bankado yadda jami'ai na kasashe 54 da za su shiga gasar, suke karbar cin-hanci kafin su sayar da tikitin ga masu son kallon wasan.

'Yan jaridar Sunday Times, wadanda suka yi sojan-gona a matsayin 'yan ka-yi-na-yi daga Gabas Ta Tsakiya, sun sayi tikiti daga kasashen Serbia da China.

Hukumar ta sanya kwamatinta da ke kula da da'a ya binciki zarge-zargen.

A watan jiya ne dai wani babban jami'i na hukumar da ke Ukraine ya sauka daga mukaminsa, bayan da BBC ta dauki hoton bidiyonsa a lokaci da yake sayar da tikitin shiga gasar a kasuwannin bayan-fage.

Karin bayani