BBC za ta fara shirin talabijin a kan Afirka

Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Tambarin BBC

A ranar Litinin ne kafar watsa labarai ta BBC za ta fara gabatar da shirin talabijin na musamman a kan nahiyar Afrika wanda a turance ake kira BBC Focus on Africa TV .

Shirin dai shi ne na farko a jerin wasu sababbin shirye-shirye da BBC za ta fito da su da za su kunshi gudummawa daga kwararrun masu aiko da rahotanni na BBC daga sassan Afrika da dama, da ma sauran nahiyoyin duniya.

Bilkisu Labaran na daga cikin Editocin sabon shirin, ta ce shirin na da fatan sauya akalar irin kallon da ake yi wa Afirka:

''Abin da muke so mu nuna a wannan shirin shi ne lokaci fa ya wuce da za a dauki Afirka ita ce nahiya wadda ta ke can wani wuri, kebantacciya; kamar ma ba a cikin duniya take ba; ana ganin mu tsiraru a gefe daya.Yanzu Afirka ita ce kan gaba''.

Ta kara da cewa sauran sassan duniya na da na su matsalolin amma ba kasafai ake jin kan su ba, don haka ya kamata Afirka ma ta bi sahun irin wadancan nahiyoyi.