Focus on Africa: Sabon shirin talabijin na BBC

Gidan talabijin na BBC
Image caption Gidan talabijin na BBC

BBC ta kaddamar da shirinta na farko kan Afirka a kafar talabijin.

Shirin wanda ake kira Focus on Africa, zai rika fita ne ta kafar talabijin BBC World News.

Fatan BBC shine, ta samu masu kallon shirin da suka kai mutane million tara a mako guda nan da dan lokaci kadan, da nufin samar da wani kari ga masu saurare ta kafar redio, wadanda aka kiyasta cewa sun kai mutane million 70.

Za ta rika watsa shirye shiryen ta ne daga cibiyonta guda hudu a Afirka wato Nairobi da Abuja da Johannesburg da kuma Dakar.

Karin bayani