Uefa ta dakatar da Bendtner saboda nuna kamfai

Hukumar kula da kwallon Turai wato Uefa ta dakatar da dan wasan Denmark, Nicklas Bendtner na tsawon wasa daya, da kuma cin tarar Euro 100,000, saboda nuna kamfai da ya yi a lokacin da ya ke murnar zura kwallo a wasan da da kasarsa ta buga da Portugal.

Dan wasan ya saukar da gutun wandon da ya sa ne inda kamfansa ya fito a lokacin da ya zura kwallo ta biyu a wasan da kungiyar ta sha kashi a hannun Portugal da ci uku da biyu.

"Dakatarwar da aka yiwa dan wasan za ta fara aiki ne a wasanni share fage na taka leda a gasar cin kofin duniya ta shekara ta 2014." In ji Uefa.

Bendtner na da kwanaki uku na daukaka kara game da batun.

Akwai dai sunnan kamfanin da aka rubuta a kamfan da dan wasan ya sa, wanda kuma ake zarginsa da tallatawa.

Bendtner dai ya musanta cewa ya aikata ba dai-dai ba, inda ya ce bai san yana karya doka bane a lokacin da ya yi hakan.