Ana shirin kafa gwamnatin-hadaka a Girka

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Antonis Samaras

A kasar Girka, jam'iyyun da ke goyon bayan matakin tsuke-bakin-aljihun gwamnati sun fara tattaunawa a kan yadda za su kafa gwamnatin gamin-gambiza bayan da jam'iyar New Democracy ta lashe zaben da aka gudanar ranar Lahadi.

Shugaban jam'iyyar, Mista Antonis Samaras, ya shaidawa magoya bayansa cewa zai cigaba da mutunta yarjejeniyar da kasar ta amince da ita ta ceto tattalin arzikin kasar bisa sharudan kungiyar Tarayar Turai.

Ya lashe zaben ne da kyar domin kuwa tazarar da ya bai wa abokin hamayyarsa ba ta da yawa.

Sai dai nasarar ta bai wa jam'iyar damar samun karin kujeru hamsin a Majalisar Dokokin kasar Girka.

Kasashen duniya sun yi murna da zaben

Mista Samaras ya yi kira ga sauran jam'iyun da su hada kai da shi domin ceto tattalin arzikin kasar daga durkushewa:

'' A yau, al'umar kasar Girka sun bayyana amincewarsu ta cigaba da kasancewa cikin kasashen da ke amfani da kudin Euro, lamarin da zai sanya a samu dawwamammen cigaba .Wannan nasara ce ga kafatanin kasashen Turai.Ina kira ga dukkan jam'iyun da ke da irin ra'ayina da su zo mu hada gwiwa don samar da sabuwar gwamnati mai dorewa''.

A cewar Mista Samaras, gwamnatinsa za ta hada gwiwa da kasashen Turai wajen ganin tattalin arzikin Girka ya bunkasa.

Sai dai shugaban jam'iyyar Syriza mai son kawo sauyi, Alexis Tsipras, ya jaddada matsayin jam'iyar na adawa da matakan tsuke bakin aljihu.

Kasuwannin hannun jari da shugabannin kasashen duniya dai sun yi na'am da sakamakon zaben na Girka.

Karin bayani