Gwamnatin Girka na neman mafita

Antonis Samaras Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Shugaban jam'iyyar da ta ci zabe a Girka

Shugaban jamiyyar New Democracy masu matsakaicin ra'ayin rikau a kasar Girka, ya ce kasar na bukatar sabuwar gwamnatin rikon kwarya cikin gaggawa.

Antonis Samaras na magana ne kwana guda bayanda jamiyyarsa ta samu nasara da kankanin rinjaye a babban zaben kasar mai muhimmanci ga makomar Girka a tarayyar turai.

Antonis Samaras ya ce ba tare da wata wata ba zai yi kokarin kafa gwamnatin da za ta ceto kasar tare da sauran jamiyyun siyasa da suka yi imani da manufofin turai da kudin bai daya na euro.

Karin bayani