Sojin Masar sun kwace ikon yin dokoki

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Shugaban Majalisar Sojin Masar, Mohammed Tantawi

Majalisar Mulkin Sojin Masar ta bayar da sanarwar karbe ikon shimfida dokoki da kuma yin kasafin kudi.

Majalisar ta dauki wannan mataki ne a yayin da Misrawa ke jiran sakamakon zaben shugaban kasar.

Ana hasashen sanarwar da za a yi bayaninta filla-filla a ranar Litinin za ta ce babu damar sake gudanar da zaben majalisar dokoki sai bayan sauya tsarin mulkin kasar.

A na ta bangaren, kungiyar 'yan uwa Musulmi ta ce dan takararta, Muhammad Mursi, ne ya lashe zaben shugaban kasar, kodayake sai nan da mako guda ne za a fitar da sakamakon a hukumance.

Sabon shugaban kasar zai fuskanci kalubale da dama, babban cikinsu kuwa shi ne tabbatar da nasarar mika mulki ga farar hula daga sojojin da ke neman mamaye kowanne bangaren rayuwa a Masar.

Karin bayani