An kashe fiye da mutane 20 a Damaturu

Hakkin mallakar hoto AFP

Kungiyar agaji ta Red Cross ta ce mutane fiye da ashirin ne ta samu tabbacin cewa sun rasu sakamakon dauki ba dadin da aka yi tsakanin jami'an tsaro da mayakan kungiyar Boko Haram Damaturu dake arewa maso gabashin Najeriya.

Wani kakakin kungiyar agaji ta Red Cross ya ce: "Yanzu dai ya kusan kai mutane ashirin wadanda muka gani, amma wasu din da dama bamu san wala-Allah ko ba a shiga lunguna ba, ko kuma ba a iya adadin da aka samu ke nan.

"Akwai fararen hula, akwai kuma jami'an tsaro guda ukku".

Tuni dai aka sanya dokar hana zirga zirga ta sa'o'i ashirin da hudu a biranen Damaturun da Kaduna inda mutane fiye da hamsin suka rasu a ranar Lahadi sakamakon rikici tsakanin Musulmai da Kirista.

Karin bayani