An shiga rudanin siyasa a Pakistan

Yusuf Raza Gilani Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Yusuf Raza Gilani

Kotun kolin Pakistan ta haramta wa Pira ministan kasar Yusuf Raza Gilani ci gaba da rike mukaminsa.

Kotun ta ce ta yanke wannan hukunci ne saboda ta same shi da laifi, sakamakon tuhumar da aka yi masa ta rena kotun a cikin watan Aprilun da ya gabata, bayan da ya ki ya sake kaddamar da bincike kan zargin cin hancin da ake yiwa shugaban kasar, Asif Ali Zardari, akan na cin hanci da rashawa kan shugaban kasar.

Wakiliyar BBC ta ce, wannan hukunci na nufin za a sake shiga cikin rudanin siyasa a kasar a daidai lokacin da dangantaka tsakanin Pakistan da Amurka ke cikin wani mawuyacin hali.

Wannan hukuncin kotun dai shi ne na baya bayan nan a jerin fito na fito tsakanin bangaren sharia da yan siyasar kasar.

A wani labarin kuma an harbe wata shahararriyar mawakiya a arewa maso yammacin Pakistan har lahira.

Wasu yan bindiga ne akan babur suka halaka Ghazala Javed da mahaifinta a Peshawar.

Yan sanda sun ce kisan na da alaka da takaddama ta yan uwa.

Ms Javed ta yi aure shekaru biyu da suka gabata, to amma daga bisani ta koma gidan mahaifanta sannan ta nemi rabuwa da mijin.

Ta na waka ne a harshen Pashto kuma ta fito ne daga yankin Swat.

A lokacin da kungiyoyin Islama suka mamaye yankin, akwai lokacin da aka yi wa Ghazala Javed barazana ga rayuwarta, inda aka hana ta waka.

Karin bayani