An kafa dokar hana fita a Kaduna da Damaturu

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Hare-hare a Najeriya

Gwamnatin jihar Kaduna ta sake kafa dokar hana fita na sa'oi ashirin da hudu biyo bayan barkewar tashin hankali a wasu sassa a garin Kaduna.

Jama'a sun yi ta guje-guje bayan da rikici ya bulla a wadansu unguwanni inda Musulmi ke da rinjaye.

Hakan dai ya biyo bayan wadansu rahotanni na tashin hankali da aka ce an samu jiya a wadansu unguwanni na birin na Kaduna inda Kiristoci suka fi rinjaye.

Rahotanni sun ce hayaki ya yi ta tashi a wadansu wurare sanadiyyar kone-kone.

Kawo yanzu dai babu cikakken bayani a kan irin barnar da rikicin na yau ya haifar.

Hakazalika a jihar Yobe Gwamnati ta bada sanarwar sanya dokar hana fita na sa'oi shirin da hudu a cikin garin Damaturu sakamakon halinda ake ciki

Rahotanni sun ce mazauna garin Damaturun na cikin hali na tsoro sakamakon tashin bama bamai da karar bindigogi babu kakkautawa da sukai ta ji a wasu sassan birnin da yammacin jiya.

A halinda ake ciki dai kusan za'a ce komai ya tsaya cik a garin na Damaturu sakamakon dokar hana fita da gwamnatin ta yi shelar sakawa.

Galibin mazauna garin Damaturun dai a yanzu na zaune a cikin gidansu kuma wuraren kasuwanci sun kasance a rufe.

Dangane da yawan mutanen da suka rasu ko wadanda suka jikkata, wani babban jami'in hukumar bada agaji ta red cross Alhaji Zabu Buba ya shaidawa BBC cewa har ya zuwa safiyar yau anyi ta jin karar harbe harbe a Damaturun domin haka suna nan suna jiran sai komai ya lafa kafin su fita aiki.

Tashe tashen hankula na baya bayannan na cigaba da jan hankulan Kasashen duniya domin ko a yau wata sanarwa data fito daga jakadar Kasashen turai da kuma tsaro Catherine Ashton, tace ta kadu matuka da hare- haren da aka kaiwa coci a Najeriya da wadanda suka zo kafin wannan kuma tace tayi Allawadai da wadannan tashe -tashen hankula da suke janyo asarar rayuka.

Ta kuma ce tarayyar turai zatai aiki da gwamnatin Najeriya wajen kawo karshen matsalolin da yankin arewacin kasar ke fuskanta

.

Karin bayani