An kafa dokar hana fita a Kaduna da Damaturu

Hari kan coci Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Hare-hare a Najeriya

Gwamnatin jihar Kaduna da ke arewacin Najeriya ta sake kafa dokar hana fita ta sa'oi ashirin da hudu sakamakon barkewar tashin hankali a wasu sassa a garin Kaduna.

Hakazalika a jihar Yobe gwamnati ta bada sanarwar sanya dokar hana fita ta sa'oi shirin da hudu a cikin garin Damaturu sakamakon hare-haren da wasu 'yan bindiga suka kai garin.

Rahotanni sun ce mazauna garin Damaturun na cikin halin tsoro sakamakon tashin bama-bamai da karar bindigogi babu kakkautawa da suka yi ta ji a wasu sassan birnin da yammacin jiya.

A halinda ake ciki dai kusan za'a ce komai ya tsaya cik a garin na Damaturu sakamakon dokar hana fita da gwamnatin ta yi shelar sakawa.

Galibin mazauna garin Damaturun dai a yanzu na zaune a cikin gidajensu kuma wuraren kasuwanci sun kasance a rufe.

Dangane da yawan mutanen da suka rasu ko wadanda suka jikkata, wani babban jami'in hukumar bada agaji ta Red Cross Alhaji Zabu Buba ya shaidawa BBC cewa har ya zuwa safiyar yau an yi ta jin karar harbe-harbe a Damaturun domin haka suna nan suna jiran sai komai ya lafa kafin su fita aiki.

Sai dai kwamishinan 'yan sanda na jihar Mr Patrick ya ce ba zai iya tabbatar da adadin wadanda suka mutu ba, amma 'yan sanda uku sun rasa rayukansu yayinda wasu hudu suka samu raunuka.

Tashe- tashen hankula na baya bayan nan na ci gaba da jan hankulan Kasashen duniya domin ko a yau wata sanarwa da ta fito daga jakadar Kasashen turai Catherine Ashton, ta ce ta kadu matuka da hare- haren da aka kaiwa coci-coci a Najeriya da wadanda suka zo kafin wannan kuma ta ce ta yi Allawadai da wadannan tashe -tashen hankula da suke janyo asarar rayuka.

Ta kuma ce Tarayyar Turai za ta yi aiki da gwamnatin Najeriya wajen kawo karshen matsalolin da yankin arewacin kasar ke fuskanta.

.

Karin bayani