An shafe daren jiya ana artabu a Afghanistan

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Afghanistan

Ana cigaba da fafatawa kusa da Kabul babban birnin Afghanistan inda mayakan Taliban suka kai hari kan wani otal tun daren jiya.

'Yan sanda sun ce sun kashe uku daga cikin maharan yayinda biyu ke cigaba da barin wuta.

Haka kuma an kashe masu gadi biyu da dansanda daya. Kodayake an ceto mafi yawan mutanen da maharan su ka yi garkuwa da su.

Sojojin Afghanistan sun tunkari yan bindigar inda akai ta musayar wuta. An dai fara artabun ne a daren jiya Alhamis yayinda wasu masu hannu da shuni yan Afghanistan din suka hallara a hotel din don yin party.

A ranar talatar da ta gabata a wani harin kunar bakin wake mutane akalla ashirin da daya sun mutu har da sojin Amurka uku.

Karin bayani