An yankewa Umar Patek hukuncin daurin shekaru ashirin

Umar Patek a kotu Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Umar Patek a kotu

Wata kotu a Indonesia ta yankewa mutumin da ake zargi ya jagoranci hada bama-baman da aka tayar a Bali a shekara ta 2002, hukuncin daurin shekaru 20 a gidan kaso.

Alkalan kotun sun sami Umar Patek da laifukan kisa da hada bam dake da alaka da hare -haren da aka kai wasu gidajen rawar disco a Bali, wanda ya hallaka sama da mutane dari biyu.

Masu shigar da kara dai ba su nemi a yanke ma sa hukucin kisa ba bayan da ya yi ta neman afuwar laifukan da ya aikata a lokacin shari'ar.

Umar Patek dai ya kasance daya daga cikin mutanen da aka nema ruwa jallo a kasar Indonesia kafin a kama shi a kasar Pakistan a bara.

Karin bayani