Hukumar Moody's ta rage darajar manyan Bankuna

Image caption Euro

Hukumar kimanta karfin biyan basussuka ta kasa da kasa ta Moody's ta rage darajar karfin biyan bashin sha biyar daga cikin manyan bankunan duniya, ciki kuwa har da Goldman Sachs, da Credit Suisse, da Deutsche Bank da kuma Barclays.

Matakin na zuwa ne lokacin da ake cikin rudani dangane da kasashen da ke amfani da kudin Euro, da dakushewar tattalin arzikin Amurka, da kuma kasashe masu tasowa.

Wakilin BBC yace matakin da hukumar Moody's ta dauka ya yi matukar rage kimar bankunan kuma zai ja musu karin kudin ruwan da za su biya wurin karbar bashi.

Yankin turai dai na fama da yunkurin farfado da tattalin arzikinsu.

Karin bayani