An ji karar harbe harbe a Kano

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Good luck Jonathan

Rahotanni na cewa mazauna yankin Dorayi dake jihar Kano sun ce sun ji karar fashewar wasu abubuwa a daren jiya, lamarin da ya haddasa firgici ga jama'a.

Karar fashewar abubuwan ya biyo bayan harbe harbe da aka ji daga yankin da misalin karfe bakwai na yammacin jiya.

Wani da abin ya faru a kusa da gidansa ya shaidawa BBC cewa yaji karar fashewar abubuwa uku masu karfi da misalin karfe goma na daren jiya.

Hare haren bama bamai da na bindigogi na dada karuwa a yan kwanakin nan a arewacin kasar. Ko a makon da ya gabata an kai harin bama-bamai a Jihar Kaduna abinda ya haifar da ramuwar gayya a wasu sassan Jihar.

Karin bayani