Hukumar zaben Masar ta jinkirta fadin sakamako

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Morsi da Shafiq

Hukumar zaben Masar ta jinkirta bayyana wanda ya lashe zaben shugaban kasar, bisa hujjar cewa, tana bukatar karin lokaci domin duba koke-koke da aka gabatar mata dangane da zaben.

Yau ne dai ya kamata a bayyana sakamakon zagaye na biyu na zaben shugaban kasar da aka fafata tsakanin dan takarar kungiyar 'yan uwa musulmi, Muhammed Mursi da kuma tsohon Prime Ministan kasar, Ahmed Shafiq

Wata gidan talabijin ta gwamnatin kasar ta ambato Hukumar zaben kasar na cewa ta samu korafe korafe sama da dari hudu daga yan takarar shugaban kasar su biyu.

Wannan ne inji hukumar zaben ya sa za a jinkirta bada sanarwar sakamakon zaben har sai an yanke hukunci kan korafe korafen da yan takarar biyu suka gabatar.

A yau ne dai da farko aka shirya zaa sanar da sakamakon zaben abunda yan kasar suke ta zumudin saurara.

Sai dai wannan matsayar ta hukumar zaben da ta dauka na zuwa ne a lokacin da bangarorin biyu ke ikirarin lashe zaben wanda akayi zagaye na biyu a karshen mako.

Karin bayani