Sudan da Sudan ta kudu za su koma tattaunawa

Image caption Sudan kusini

Yau ne ake saran Sudan da Sudan ta kudu zasu koma kan teburin tattaunawa domin warware takaddama akan iyakokinsu da ta kusan kai su ga afkawa cikin yaki a watan Aprilun da ya gabata.

Tattaunawar da za'a yi a Ethiopia zata maida hankali ne ga tantance hakikanin iyaka tsakanin kasashen biyu ta yadda za'a kafa shinge tsakaninsu

Wakilin BBC yace kasashen Sudan da Sudan ta kudun na yin jayayya ne akan wasu muhimman batutuwa ne da ya kamata a warware su tun ma kafin Sudan ta kudu ta balle, batutuwan kuma sun hada ne da batun arzikin mai, da kuma tsaro.

Sudan ta kudu ta samu cin gashin kanta ne ba tare da warware matsalolin iyaka ba da kuma yankin dake da arzikin man fetur, wadanda suke samun sabani a kai.

Karin bayani