Amurka ta ayyana wasu shugabannin Boko Haram a matsayin 'yan ta'adda

Abubakar Shekau Hakkin mallakar hoto youtube
Image caption Abubakar Shekau

Gwamnatin Amurka ta ayyana wasu mutane uku da take zargin cewa na daga cikin manyan shugabannin kungiyar Jama'atu Ahlissunnah Lidda'awati wal jihad da aka fi sani da Boko-haram a matsayin 'yan ta'adda na ketare tare da rufe asussansu da kame kadarorinsu da ke Amurka idan suna da su.

Mutum uku da gwamnatin Amurkar ta ayyana a matsayin 'yan ta'addan, an yi amanna cewa na daga sahun gaba-gaba a tsakanin shugabannin kungiyar Boko Haram, wadanda suka hada da Imam Abubakar Shekau da Abubakar Adam Kambar da kuma Khalid al-Barnawi, wadanda kuma dukkansu 'yan Najeriya ne.

Ayyana wadannan jagororin Kungiyar a jerin 'yan ta'adda, za ta yi sanadin kame dukkan kadarorin da suka mallaka a Amurka, tare da haramta musu yin kowace irin hulda da Amurkawa.

Masu sharhi a kan al'amura na ganin cewa, a zahiri wannan matakin ba zai yi wani tasiri na kai tsaye, sai dai wani mataki ne da gwamnatin Amurka ke yi na kawo karshen tashe-tashen hankulan da ake dangantawa da kungiyar ta Boko Haram.

Wannan mataki da Amurka ta dauka ya biyo bayan matsin-lambar da gwamnatin Obama ke fuskanta ne game da bukatar gaggauta daukan mataki a kan kungiyar Jama'atu Ahlissunnah Lidda'awati wal jihad.

Tattaunawar Sulhu

Kuma shi ne mataki na farko da gwamnatin Amurkan ta dauka a kan kungiyar.

Kodayake a hakan ma matakin ya saba da bukatar wasu 'yan majalisar kasar wadanda ke ganin kamata ya yi a sanya kungiyar ne baki dayanta a jerin 'yan ta'adda.

Kazalika wannan mataki watakila zai ci karo da ra'ayin gwamnatin Najeriya, wadda kamar yadda take ikirari har yanzu tana duba hanyoyin sulhuntawa da 'yan kungiyar.

Su ma 'yan Najeriyar da dama na da ra'ayin cewa tattaunawar sulhu da 'yan kungiyar ita ce kawai mafita, kamar yadda dattawa da matasa, musamman daga arewacin kasar ke fitowa da sunan kungiyoyi daban-daban suna yin wannan kiran.

Sai dai kungiyar Jama'atu Ahlissunna lidda'awati wal jihad a nata bangaren, cikin wata sanarwar da shugabanta Imam Abubakar Shekau ya yi kwanan baya ya ce ta rufe kofar sulhuntawa da gwamnati, bisa zargin cewa ba a cika mata wasu sharudanta ba, kodayake 'yan magana kan ce baya ba ta kadan.

Karin bayani