Ya kamata a saka Iran cikin warware matsalar Syria

annan Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Mista Kofi Annan

Wakilin Majalisar Dinkin Duniya, Kofi Annan, ya ce ya yi amannar cewa kamata ya yi a saka Iran cikin kokarin kawo karshen rikicin Syria.

Mista Annan ya gaya wa taron manema labarai a Geneva cewa yana son a sanya kasashe masu karfin fada-a-ji da ke goyon bayan bangarorin biyu cikin tattaunawar.

Kuma ya yi amannar cewa a saka Iran a cikinsu.

Ya ce, "Muna tattaunawa akan wadanda za su shiga cikin batun. Amma na bayyana a sarari sosai cewa na yi amannar cewa a sanya Iran a cikin shirin."

Amurka dai tana adawa sosai da batun saka Iran cikin tsarin samar da zaman lafiya a Syriar.

Karin bayani