Sambo Dasuki ne sabon mai baiwa shugaban Najeriya shawara a harkar tsaro

Shugaban Najeriya Goodluck Jonathan Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Shugaban Najeriya Goodluck Jonathan

Gwamnatin Najeriya ta nada Sambo Dasuki a matsayin sabon mai baiwa shugaban kasar shawara a kan harkokin tsaro tare da sauke ministan tsaron kasar daga mukaminsa.

Sambo zai maye gurbin tsohon mai bada shawara ga shugaban kasar ne Janar Andrew Azazi.

Kazalika gwamnatin ta sanar da sauke ministan tsaron kasar, Dr Bello Halliru daga mukaminsa, amma ba ta sanar da wanda zai maye gurbinsa ba.

Gwamnatin ta dauki wannan matakin ne a taron majalisar tsaron kasar, wanda shugaba Goodluck Jonathan ya jagoranta yau din nan.

Kawo yanzu dai gwamnatin ba ta fadi dalilin sauke Janar Azazin da Dr Bello Halliru daga mukaman nasu ba.

Karin bayani