'Yan Muslim Brotherhood sun hallara a dandalin Tahrir

tahrir Hakkin mallakar hoto AP
Image caption 'Yan Muslim Brother a dandalin tahriri

Magoya bayan jam'iyyar 'Yan'uwa Musulmi ta Ikhwanul Muslimin a Masar, sun sake hallara a Dandalin Tahrir a Alkahira bayan sallar Juma'a.

Sun sha alwashi cewa za su zauna a wurin har sai an bayyana sakamakon zaben shugaban kasar da aka yi a karshen makon amma aka yi jinkirin bayyanawa.

Rahotannin da ba hukumomi ne suka bayar da su ba, sun nuna cewa dan takarar 'Yan'uwa Musulmin ne, Mohammed Morsi, ya lashe shi.

Sai dai abokin hamayyarsa, tsohon piraminista, Ahmed Shafiq, ya musunta hakan.

Karin bayani