"A yanke hukunci Breivik ba mahaukaci ba ne"

Anders Behring Breivik Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Anders Behring Breivik a rana ta karshe ta sauraron kararsa

A karshen makwanni goma da aka kwashe ana shari'a a Norway, lauyoyin da ke kare Anders Behring Breivik sun mika bukatunsu na karshe a shari'ar da ake yi masa, inda suka nemi mai shari'a ya yanke hukuncin cewa yana da hankali, kana ya aika da shi gidan yari.

Ya dai amsa kashe mutane saba'in da bakwai, galibinsu 'yan shekara goma-sha.

Wadanda suka tsira da ransu da kuma 'yan uwan wadanda ya kashe a watan Yulin bara sun fice daga cikin kotun a lokacin sauraron shari'ar a rana ta karshe.

Wani bawan Allah mai suna Trond Henry Blattmann na cikin wadanda aka kashe masu 'ya'ya a lokacin harbin da Mista Breivik ya yi.

A cewarsa, "Muna so a daure shi daurin ra-da-rai a inda al'ummar kasar Norway za su iya ganinsa - abin da ya kamata a yi masa ke nan; kalamansa a cikin makwanni goman da suka wuce sun nuna cewa bai yi da-na-sani ba".

Lauyoyin da ke kare Mista Breivik din sun ce dan ta'adda ne, amma dalilan ta'addancinsa na siyasa ne, don haka laifin da ya aikata yana wuyansa - ya san ba daidai ba ne kashe mutum, amma ya zabi aikata hakan.

Babban lauyan da ke kare Mista Breivik, Geir Lippestad, ya bayyana cewa: "Ya kamata wanda muke karewa ya amfana da irin hukuncin da ya dace a yanke masa. Idan kuma aka yi la'akari da bayanan wata likitar kwakwalwa, dole ne a dauki Breivik a matsayin mai cikakkiyar lafiya wanda ba shi da tabin hankali".

Sai dai masu gabatar da kara suna so a yanke hukuncin cewa mahaukaci ne, don haka a tura shi gidan mahaukata.

Bayan sauraron bukatun lauyoyin gwamnati da kuma masu kare Anders Behring Breivik dai, alkalin ya ajiye ranar 24 ga watan Agusta a matsayin ranar da zai yanke hukunci.