Jirgin saman yakin Turkiya ya bace akan iyakar kasar da Syria

Recep Tayyip Erdogan Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Recep Tayyip Erdogan na Turkiya

Firaministan kasar Turkiya, Recep Tayyip Erdogan, ya ce har yanzu bai da tabbaci a kan ko jirgin saman yaki na kasar, wanda ya bata can baya a yau, harbo shi aka yi ko kuma faduwa ya yi.

Jirgin saman yakin na Turkiya, kirar F-4, an daina ganin shi a na'urar hangen jiragen sama a kusa da kan iyaka da kasar Syria.

Kafar watsa labarai ta Lebanon, wadda a lokuta da dama akan dogara da rahotanninta, ta ambaci majiyoyin tsaro na Syria suna cewa su ne suka harbo jirgin saman.

Firaminista Erdogan yana jagorancin wani taron gaggawa na tsaro tare da shugabannin soji na Turkiyar.

Har yanzu jiragen ruwan Turkiya da Syria suna can suna neman jirgin saman da matukansa guda biyu.

Karin bayani