'Yan sanda na zanga zanga a Bolivia

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Yan sandan Bolivia

Dubban jami'an 'yan sandan kasar Bolivia na gudanar da zanga zanga a dukkan fadin kasar kan batun karin albashi, lamarin daya tilastawa shugaban kasar Evo Morales katse ziyarar da yake yi a kasar Brazil domin ya tunkari matsalar.

A ranar Alhamis ne dai tarzoma ta barke a birnin La Paz na kasar bayan da wasu jami'an 'yan sanda da dama suka kwace iko a wani barikin 'yan sanda dake kusa da fadar shugaban kasa.

Daga bisani zanga zangar ta bazu zuwa wasu biranen kasar inda jami'an 'yan sandan suka yi ta kone konen gine-gine.

Wani Ministan gwamnatin kasar Carlos Romero, ya ce Mr Morales a shirye yake ya gana da masu zanga zangar.

Karin bayani