Masu kada kuria a Masar sun mamaye Tahrir

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Tahrir square

Magoya bayan jam'iyyar 'Yan'uwa Musulmi a kasar Masar, sun ce za su ci gaba da kasancewa a Dandalin Tahrir dake tsakiyar birnin duk kuwa da gargadin da Majalisar mulkin sojin kasar ta yi na cewa ba za'a bari su kawo cikas ga harkokin yau da kullum a birnin ba.

Masu zanga zangar wadanda suka iso Dandalin bayan sallar Juma'a na bukatar a bayyana sakamakon zaben shugaban kasar da aka yi a karshen mako ne amma aka yi jinkirin sanar da sakamakon zaben.

Wasu rahotannin da ba hukumomi ne suka bayar da su ba, sun nuna cewa dan takarar 'Yan'uwa Musulmin ne, Mohammed Morsi, ya lashe shi.

Sai dai abokin hamayyarsa, tsohon Firaminista, Ahmed Shafiq, ya musunta hakan.

Karin bayani