An tsige shugaban kasar Paraguay

Hakkin mallakar hoto s
Image caption Paraguay

Majalisar dattawan kasar Paraguay sun tsige shugaban kasar Fernando Lugo daga karagar mulki.

An zargi shugaban kasar ne a rawar daya taka wajen sa ido aikace aikacen jami'an 'yan sanda masu koran wasu kananan manoma daga wani gandun dajin da aka killace a makon daya wuce, lamarin daya haddasa mutuwar mutane goma sha bakwai.

Mr Lugo wanda shine shugaban kasar na farko daga bangaren masu ra'ayin rikau ya ce ya amince da kuri'ar tsige shi da 'yan Majalisun suka kada, koda yake ya ce an jujjuya dokar da aka yi amfani da ita wajen tsige shi.

Tuni aka rantsar da mataimakinsa Federico Franco,mai matsakaicin ra'ayi a matsayin shugaban kasar domin ya kammala wa'adin mulkin.

Karin bayani