Syria ta harbo jirgin Turkiyya

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Haddad, Syria

Kasar Syria ta amince cewa ita ce ta harbo wani jirgin saman yaki na kasar Turkiyya a kusa da kan iyakar kasashen biyu.

Sojojin Syrian sun ce an harbo jirgin ne a jiya Juma'a bayan da suka zaci cewa jirgin na shirin kaiwa kasar hari ne lokacin da ya shigo sararin samaniyan Syrian, kafin daga bisani aka gano cewar jirgin yakin kasar Turkiyya ne.

Bayan wani taron gaggawa da Firaministan kasar Turkiyyan, Rajip Tayyip Erdowan ya jagoranta, kasar Turkiyyan ta ce nan bada jimawa bane zata yanke shawarar matakan da zata dauka bayan ta tattara dukkanin bayanai game da ainihin wurin da aka harbo jirgin.

Jiragen ruwa daga kasashen biyu na ci gaba da bincike da kuma kokarin ceto matukan jirgin su biyu.

Karin bayani