'Yan kasar Masar na dakon sakamakon zabe

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Masu zanga zanga

Dubban 'yan kasar Masar ne suka shafe daren Asabar a dandalin Tahrir suna zanga-zanga yayin da za a bayyana sakamakon zaben da aka dauki tsawon lokaci ba a bayyana ba na zaben raba gardama na shugaban kasar wanda za a sanar a yau Lahadi.

Yawancin mutanen dai magoya bayan dan takarar jam'iyyar 'yan uwa musulmi ne Mohammed Mursi.

Sai dai masu marawa Ahmed Shafiq baya na yin nasu dandazon suna daga tutar kasar.

'Yan takarar biyu duka dai sun yi ikirarin lashe zaben sai dai sun yi alkawarin aiwatar da gwamnatin hadin kan kasa.

Sanar da sakamakon zaben gami da bada mulkin ka iya dakatar da zanga zangar da ake yi a Tahrir Square, sai dai akwai far gaba kuma da ake yi cewa sakamakon zai iya zafafa siyasar kasar.

Karin bayani