An bayyana Mohammed Mursi a matsayin sabon shugaban Masar

Mohammed Mursi Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Mohammed Mursi na jam'iyyar 'yan uwa musulmi ya lashe zaben Shugabancin Kasar Masar

Hukumar zaben Kasar Masar ta bayyana sunan Mohammed Mursi na jam'iyyar 'yan uwa musulmi a matsayin sabon Shugaban Kasar.

Shugaban hukumar zaben Kasar Farouk Sultan shine ya ya bayyana sakamakon zaben dazu.

Shugaban Mursi mai shekaru 60 a duniya, injiniya ne da yai karatunsa a Kasar Amurka.

Ya kuma taba zama dan majalisar dokoki mai zaman kansa daga shekarar 2000-2005.

Jamiyyar 'yan uwa musulmi ta tsaida shi a matsayin dan takarar ta bayan da aka hamamtawa khairat Al- Shater tsayawa takarar zaben Shugabancin Kasar

Mohammed Mursi dai ya jinjinawa bangaren shari'ar kasar saboda gaskiyar da yace sun nuna da kuma adalci.

Ya kuma nuna godiyarsa ga 'yan sanda da sojoji wadanda yace sun kare tsarin damukradiya tare da girmama tsarin

Tuni dai shima shugaban Mulkin sojin kasar Field Marshal Mohammed Hussein Tantawi ya taya Mohammed Mursi murnar nasarar da ya samu

Tun bayan bayyana sakamakon zaben Dubun dubatar jama'ar da sukai dafifi a dandalin Tahrir suka shiga shewa da bukukuwa ta hanyar kade kade da raye raye

Yankin zirin Gaza ma dai rahotanni sunce ba a barsu a baya ba, wajen gudanar da bukukuwan nasarar Mohammed Mursi

A zirin Gaza ma, Jama'a sun yi ta kwarara kan tituna cikin farin ciki da murna. Haka kuma 'yan bindiga sun yi ta harbi cikin iska, an kuma sanya kiran sallah a masallatai tare da nuna yabo ga Ubangiji

Mai magana da yawun Falastinawa Sami Abu Zuhri ya bayyana nasarar Mohammed Mursi a matsayin wani mahimmin lokaci a tarihin Kasar, ya na mai cewa suna fatan nasarar zata inganta dangantaka tsakanin Falastinawa da Misrawa

Karin bayani