An kai harin bom a Bauchi

Hakkin mallakar hoto s
Image caption Wani waje da aka kaiwa hari a Najeriya

Wani bom ya fashe a garin Bauchi da ke arewacin Nijeriya ranar Lahadi da dare inda ya jikkata mutane da dama.

Hukumomin tsaro sun ce bom din ya fashe ne a kusa da wata mashaya da coci-coci da ke wata unguwa mai suna Bayan Gari.

Alhaji Adamu Abubakar, sakataren kungiyar agaji ta Red Cross, ya ce bom din ya jikkata mutane tara cikinsu har da yarinya 'yar watanni uku.

Kwamishin 'yan sandan jihar, Muhammad Ladan, ya ce babu wanda ya mutu sakamakon harin bom din.

Ya kara da cewa har yanzu ba a san wanda ya dasa bom din ba.