Tsohon Shugaban Nijar na adawa da matakin soji a Mali

Mali

Tsohon shugaban kasar Nijar, Alhaji Mahamane Ousmane ya ce hanyar sulhu ita ce ta fi dacewa wajen kawokarshen rikici a Mali.

Malam Mahamane Ousmane ya yi kira ga kasashen da ke makwabata da Nijar da sauran kungiyoyi irinsu CEDEAO da Tarayyar Afrika da su taimaka a samu hanyoyin sasantawa cikin ruwan sanyi domin shawo kan matsalar kasar ta Mali.

Tsohon shugaban ya bayyana amfani da karfin soja a matsayin wata mummunar hanya da zata iya janyo mummunan cikas ga kasar ta Mali da ma makwabtanta.

Rikicin na Mali wanda ke da nasaba da rikicin Libya ,matsala ce ta cikin gida da ta hada da siyasa da tattalin arziki da zamantakewa.

Tsohon shugaban na Nijar ya yi wannan furucin ne a wajen wani taron manema labarai a Yamai.

Karin bayani