Mutane hudu sun mutu a harin da aka kai a Kano

Hari a kan ofishin 'yan sanda na Sharada a Kano
Image caption Harin da aka kai a kan ofishin 'yan sanda na Sharada a Kano

Akalla mutane hudu ne suka rasa rayukansu ciki har da dan sanda daya a wasu hare-hare da aka kai ranar Talata da yamma a ofishin 'yan sanda na Dala da ke birnin Kano.

Mazauna unguwar dai sun ce an shafe sama da mintuna ashirin ana musayar wuta tare da fashewar abubuwa tsakanin 'yan sanda da maharan.

Haka kuma an kai wani harin a ofishin 'yan sanda na Panshekara da ke kudu maso yammacin birnin inda aka dauki lokaci mai tsawo ana harbe-harbe da kuma jin fashewar abubuwa.

A ofishin 'yan sanda na Dala, ’yan bindigar sun yi ta harbi da jefa nakiyoyi.

Maharan sun tsere

Wata majiya ta jami'an tsaro ta shaidawa BBC cewa kimanin mutane 30 ne suka kai harin, tana mai cewa jami'an tsaro sun kashe uku daga cikin maharan , yayin da wasu kuma suka tsere da raunin harbin da aka yi musu.

Haka kuma majiyar ta ce an kashe dan sanda daya da kuma jiwa wani rauni. Sai dai har yanzu rundunar 'yan sandan jihar Kano ba ta kai ga bayyana irin asarar rayuka ko jikkata da aka samu sakamakon harin ba.

Baya ga musayar wutar da aka yi dai an kuma rika jin karar fashewar abubuwa a wajen da aka kai harin tun daga misalin karfe shida har kusan karfe 11 na daren ranar Talata.

Ba a gama da batun harin na Dala ba kuma sai aka kai wani harin makamancin sa a barikin 'yan sanda da ke unguwar Panshekara da ke arewa maso yammacin birnin na Kano, inda mazauna yankin su ka ce da misalin karfe Takwas na dare sun ji karar fashewar wasu abubuwa sannan kuma harbe-harbe da ci gaba da fashewar abuwan suka biyo baya, abinda yasa jama'a su ka gudu suka bar shagunansu a bude saboda tsira da ransu.

A jihar Yobe ma da ke arewa maso gabashin kasar an ji karar harbe-harbe da fashewar abubuwa a unguwar Sabon Fegi da ke garin Damaturu, sai dai daga can din ma har yanzu babu wani karin bayani na jikkata ko asarar rayuka.

Hare-hare a Taraba

Rahotanni daga jihar Taraba da ke arewacin Najeriya na cewa an kwashe sa'oi da dama na daren ranar Talata ana jin karar harbe-harben bindigogi da fashewar abubuwa da dama a garin Wukari.

Mazauna garin sun shaidawa BBC cewa tun da misalin karfe goma na dare suka fara jin karar harbe-harben.

Har yanzu dai babu cikakken bayani game da rasa rayuka ko jikkata sakamakon hare-haren.

Rundunar 'yan sandan jihar ta tabbatarwa da BBC kai hare-haren amma ta kara da cewa sai ranar Laraba za ta yi cikakken bayani game da batun.

Kungiyar Boko Haram dai ta sha kai hare-hare a arewacin kasar.

Karin bayani