NATO na yin taro a kan Syria

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Jirgin Turkiya

Jakadun kasashen kawancen tsaro na NATO za su gana a Brussels bayan da Turkiya ta bukaci su tattauna game da harbo wani jirgin yakinta da dakarun tsaron Syria su ka yi.

Wannan ne karo na biyu a tarihin kungiyar mai shekaru sittin da uku da ta ke zama karkashin wani sashin tsarin mulkinta da ya bukaci hakan idan wata kasa da ke kungiyar ta ce ta na fuskantar barazana.

Wani babban jami'in diflomasiyya na yammacin Turai ya ce a ganinsa Turkiya ko NATO ba za su dauki matakin soji ba.

Shi ma mataimakin Firayim Ministan Turkiyya ya ce kasarsa na da hakkin mai da martani amma ba ta da niyyar yaki da Syria.

Tun da fari dai, sai da Turkiya ta aikewa kwamitin Sulhu na Majalisar Dinkin Duniya wata wasika inda ta bayyana masa yadda Syria ta harbo jirgin yakinta duk da yake, a cewarta, jirgin bai keta ta sararin samaniyar Syriar ba.

Kakakin Ma'aikatar Harkoki Wajen Turkiya, Selcuk Unal, ya ce:" Babu makami a jirgin na Turkiya; hasalima yana kan hanyar sa ce ta zuwa Turkiya domin yin gwaje-gwaje kan wasu na'urorinmu da ke tsaron sararin samaniya.

Gaskiya ne cewa da farko jirgin namu ya shiga samaniyar Syria na wasu 'yan mintuna.Sai dai jami'an kula da sararin samaniyarmu sun ba shi umarnin ficewa, kuma nan take ya fice; ya shiga bangaren sararin samaniyar da ba na Syria ba ne, amma mintuna sha biyar bayan hakan sai aka harbo shi da makami mai linzami''.

Karin bayani