An gwabza fada a birnin Damascus na Syria

Fada a birnin Dimashka na Syria Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption An gwabza fada a birnin Dimashka na Syria

Bangarorin Gwamnati da na ’yan tawaye a Syria sun ce an gwabza fada tsakanin bangarorin biyu a wadansu unguwannin da ke wajen birnin Dimashkah, babban birnin kasar.

Gwamnatin Syria dai ta ce jam'ian tsaro sun hallaka wadanda ta kira ’yan ta'adda gommai a arewa maso yamma da babban birnin.

Kafafen yada labarai mallakar gwamnati sun ce ’yan tawaye masu dimbin yawa ne suka kutsa ungwar Al-Hama dake bayan birnin, inda suka yi kokarin karbe iko da wata babbar hanyar da ta nufi yamma domin su samu damar kara shigowa da makamai da mayaka.

Sun kuma a cikin wadanda aka kasha ko aka raunata har da larabawan da ba ’yan kasar ta Syria ba ne, wadanda kuma aka kama wadansunsu.

Su kuma masu fafutuka sun ce an yi ta luguden wuta lokacin da karin sojojin gwamnati suka shiga yankin kuma an raunata mutane da dama bayan wadanda aka kashe.

Masu fafutukar sun kuma ce mata biyu da yaro daya na cikin mutane kimanin talatin da aka kasha; a cewarsu duka-duka mutane tamanin ne aka kashe ranar Talata a sassa daban-daban na kasar.

Duka bangarorin biyu dai sun bayar da labaran aukuwar wani abu makamancin wannan a Douma, wata unguwar bayan gari wadda ke gabas ga babban birnin, inda aka kwashe watanni ana nunawa gwamnati turjiya.

Ga alamu dai mutane a sassa da yawa na birnin na Dimashkah sun ji fashe-fashen ababe sakamakon fadace-fadace, sai dai kuma wannan kadan ne daga cikin irin gumurzun fadan da ake a kusan kowane sashe na kasar ciki har da lardunan Deraa na kudanci, Dair az-Zur da ke gabas da kuma Idlib da ke arewa maso yamma.

A birnin Homs da ke tsakkiyar kasar da garuruwan da ke zagaye da shi ma har yanzu fagagen daga ne.

Kungiyar agaji ta Red Cross ta kasa-da-kasa da takwararta ta Red Crescent reshen Syria sun kwashe makwanni suna kokarin kwashe fararen hular da rikicin ya rutsa da su a Homs, amma kuma tsananin fadan ya hana.

Wannan dai na faruwa ne a daidai lokacin da kungiyar kawancen tsaro ta NATO ta yi tir da harbo jirgin Turkiyya da sojan Syrian suka yi ranar Jumu'a bisa dalilin cewa ya kutsa sararin samaniyar kasar ba da izini ba.

Sai dai kuma ma’aikatar harkokin wajen Rasha ta ce saukar da jirgin ba tsokanar fada ba ce kamar yadda wadansu ke gain, sannan ta yi gargadin kada a shigar da siyasa ko a zuzuta lamarin da farfaganda.

Karin bayani