Babban Bankin Turai ka iya samun iko kan kasafin kudi a yankin

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Shugabannin Turai

Kungiyar tarrayar Turai, EU, na duba yiwuwar bullo da wani tsari, da zai bata damar samun karfin fada aji a harkokin tattalin arzikin kasashen dake amfani da kudin bai daya na Euro.

A cikin sabon tsarin dai, za a baiwa babban bankin turai karfin lura da kasafin kudaden kasashe, da kuma tilastawa gwamnatocin Turai canza yadda suke kashe kudade, idan har sun zarta sharudan da aka gindaya.

Shugaban EU, Herman van Rompuy a ranar Alhamis zai gabatar da wannan bukata ga taron kolin kungiyar.

Wakilin BBC yace: wannan tsarin nada kalubalen siyasa ga yawancin kasashen, a yayinda jama'a ke cigaba da nuna damuwa akan batun dunkulewar kungiyar waje guda.

Nan gaba a yau ne dai, ministocin kudi na kasashen Faransa da Jamus da Italiya da kuma Spain zasu tattauna akan hanyoyin magance matsalar da kudin Euro ke ciki.

Karin bayani