NATO ta soki harbo jirgin Turkiyya

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Anders Rassmussen

Kungiyar kawance ta NATO tayi kakkausar suka akan harbo wani jirgin saman yakin Turkiya da kasar Syria ta yi.

Sakatare Janar na NATO, Anders Fogh Rasmussen, shine yayi sukar, lokacin wata tattaunawa da jakadun NATO a Brussels.

An zargi kasar ta Syria da rashin girmama dokokin kasa da kasa na zaman lafiya da tsaro.

Gwamnatin Syria dai ta ce ta harbo jirgin na Turkiyya ne saboda ya shiga sararin samaniyyar ta.

Karin bayani