Malamai sun soki Jonathan akan kayyade iyali

jonathan Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Shugaban Najeriya, Goodluck Jonathan

Shugabannin addinai a Najeriya sun soki lamirin Shugaba GoodLuck Jonathan saboda tseguntawar da ya yi cewa akwai yiwuwar zai bullo da doka ta kayyade yawan iyali.

Malamai a arewacin kasar sun ce za su yi watsi da duk wata doka da za a bullo da ita wadda za ta tilasta ma Iyaye takaita yawan yaran da za su haifa.

A cewarsu ilimantar da mutane shine mafi a'ala.

To, amma Tonte Ibraye Shugaban wata kungiya ta 'White Ribbon Alliance' dake fafutukar ganin jama'a sun kayyade yawan iyali ya gaya ma BBC cewar ya ji dadi da kalaman shugaban kasar.

Ibraye yace, "Wannan labari ne mai dadin ji. Shugaban kasar ya fara fahimtar muhimmancin maida kai ga batun kayayyade yawan jama'ar kasar".

Karin bayani