'Yan kishin Islama sun kwace garin Gao na Mali

mali Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Mayakan Islama a Mali

Rahotanni daga Mali sun ce mayakan 'yan kishin Islama masu alaka da kungiyar al-Qaeda sun kwace garin Gao dake arewacin kasar.

Mazauna garin sun ce 'yan kishin Islamar sun karbe gine-ginen da 'yan tawaye na Abzinawa suke zaune hade da hedikwatar su - suka kuma daga bakar tuuta.

Wani wakilin BBC a Mali, ya ce Abzinawa masu yawa sun arce daga garin, a yayinda aka kashe a kalla mutane ashirin.

A ranar talata an yi wani boore a titunan Bamako babban birnin kasar yayinda mutane suka rinka rera taken nuna rashin amincewa maamayar da 'yan tawayen suka yi ma arewacin kasar.

Zaman dar dar

Mazauna garin sun bada bayanai ta wayar tarho cewar suna cikin firgici saboda gungun 'yan tawayen suna bata kashi a cikin garin.

Rahotanni sun nuna cewar mutane sun zauna a cikin gida sun kasa fitowa a yayinda kuma aka rurrufe shaguna.

Shaidu sun ce anyi amfani da manyan makamai, kwana guda bayan an kashe fararen hula biyu tare da jikkata wasu da dama, sakamakon zanga zangar nuna adawa da kisan da aka yiwa wani kansilan yankin a farkon wannan makon.

Watanni uku, bayan sun kwace iko a yankin arewacin Mali, a yanzu haka ana cigaba da zaman dar dar a tsakanin mayakan Azbinawa da kuma mayaka masu kishin Islama, bayan da suka kasa kulla yarjejeniya a tsakaninsu.

Mayakan Islama wadanda ke alaka da reshen Alkaida na yankin arewacin Afrika dai suna so ne a kafa daular Musulunci a yankin, a yayinda su kuma 'yan tawayen Azbinaya na MNLA suke san a kafa wata kasa wacce bata da nasaba da tsarin addini.

Karin bayani