Sarauniya Elizabeth, ta gaisa da McGuinessna IRA

mcguiness Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Sarauniyar Ingila, Elizabeth da Martin McGuiness.

Sarauniyar Ingila, Elizabeth, ta gaisa da tsohon dan kungiyar IRA, Martin McGuiness, wanda yanzu shi ne Mataimakin Firimiyan Ireland ta Arewar.

Sun yi masafaha tare da yi wa juna murmushi a wani gidan wasan kwaikwayo a birnin Belfast.

Hakan dai wata babbar manuniya ce ta irin sake daidaitawar da aka samu a yankin tun bayan da aka soma yunkurin zaman lafiya.

Ita dai kungiyar IRA ta yi fafitika ce ta ganin Ireland ta Arewa ta balle daga Biritaniya da kuma hadewa da Jumhuriyar Ireland.

Kungiyar IRA a wani hari na ta'addanci ta hallaka dan'uwan Sarauniyar, Lord Mountbatten a shekarar 1979.

Karin bayani