Ana binciken bankuna bisa zargin cuwa-cuwa

Hakkin mallakar hoto PA
Image caption Tambarin bankin Baclays

Mahukunta a Amurka, da Turai, da kuma Asiya na binciken wasu daga cikin manyan bankunan duniya bisa zargin cuwa-cuwa game da kudin ruwan da suke caja na ba da basussuka tsakaninsu, wanda kan shafin miliyoyin masu alaka da bankuna.

Daga cikin bankunan da ake zargi har da Citigroup, da JP Morgan, da kuma Deutsche Bank.

A ranar Laraba ne dai aka ci tarar bankin Barclays mai tushe a Burtaniya dala miliyan dari hudu da hamsin da biyu.

Masu lura da aiyukan banki a Burtaniya da Amurka sun ce bankin Barclays na yin karya kan kudin ruwan da ya ke biya a kan basussukan da yaci, a wani kokarin samun kazamar riba da kuma nunawa duniya cewa bankin na da karfin jari.

Bankin dai ya amince da yin kuskure.

Karin bayani