ECOWAS za ta tattauna akan rikicin kasar Mali

rikicin kasar Mali Hakkin mallakar hoto AFP PHOTO MNLA
Image caption rikicin kasar Mali

A yau ne shugabannin kasashen yammacin Afrika wato ECOWAS za su gudanar da wani taro a kasar Ivory Coast, inda ake sa ran za su tattauna kan ricike-rikicen da ake fama da su a kasar Mali.

Taron na zuwa ne a daidai lokacin da hukumar kula da al'adu da ilimi da kimiyya ta Majalisar Dinkin Duniya wato UNESCO ke bayyana damuwa dangane da barazanar da wuraren adana kayayyakin tarihi na Mali ke fuskanta sakamakon karuwar tashe-tashen hankula a arewacin kasar.

Hukumar ta UNESCO ta ce tuni ta sanya garin Timbuktu na kasar Malin da kuma hubbaren Askia dake garin Gao na kasar a matsayin wuraren tarihin da ke fuskantar mummunar hadari.

Hakan na zuwa ne bayan da dakarun kungiyar Ansarud Deen masu tsattauran ra'ayin Islama a arewacin kasar, wadanda suka karbe garin na Gao daga hannun 'yan tawayen Abzinawa, suka umurci 'yan tawayen da su fice daga birnin Timbuktu.