Kotu ta amince da tsarin inshorar lafiya na Shugaba Obama

obama Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Shugaban Amurka, Barack Obama

Kotun daukaka kara ta Amurka, ta amince da dokar da aka zartar a baya kan tsarin sauye-sauye game da inshorar kiwon lafiya ga 'yan kasar.

Kotun tayi watsi da gardandamin da ake cewa dokar ta wuce gona da iri, wajen neman bukatar duka Amurkawa su samu inshorar lafiya.

Hudu daga cikin alkalan kotun tara ne suka yi jayayya da sakamakon hukuncin.

Dan takarar shugabancin Amurkar karkashin tutar Republican, Mitt Romney yace Amurkawa zasu biya kudade masu yawa ne sakamakon garan bawul kan al'amuran kiwon lafiya.

Romney yace '' Tsarin Obama care zai kara yawan kudaden haraji kan Amurkawa da kusan dala biliyan dari biyar."

Karin bayani