Shugaban Somalia dana Somaliland sun gana a Dubai

Sheikh Sharif Sheikh Ahmed Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Shugaban Somalia Sheikh Sharif Sheikh Ahmed da Pirayi Ministan kasar

Shugaban Somalia, Sharif Sheikh Ahmad, ya gana da shugaban yankin Somaliland da ya ayyana mulkin kansa, Ahmad Muhammad Silanyo.

Ganawar, wadda aka yi Dubai, ita ce ta farko tsakanin shugabannin biyu tun 1991, lokacin da Somaliland, yankin arewacin Somaliar, ya ayyana mulkin kansa.

Amincewar da bangarorin biyu suka yi ta su sadu kuma su tattauna ido da ido zai iya zama karshen wata doguwar tafiya.

Shugabannin biyu sun kaucewar yin magana kan wani batu mai wuyar sha'ani wato 'yancin kan Somaliland, wani mataki da zai bakantawa mutane da yawa rai a can gida Somaliya.

Mutane sun yi ta sauraron jin anyi wata 'yarjejeniyar da ke fayyace matsayin Somaliland din.

Wasu a birnin Hargeisa sun yi fatan taron ya kasance mataki na farko wajen raba kasar Somaliya.

Karin bayani