Turkiyya na jibge sojoji a iyakarta da Syria

Ayarin motocin Turkiyya dauke da tankunan yaki Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Ayarin motocin Turkiyya dauke da tankunan yaki sun nufi kan iyaka

Gwamnatin Turkiyya ta ce za ta kara karfin sojinta da ke kan iyakar kasar da Syria.

An dai ga jerin motocin sojin Turkiyyar kusan talatin suna barin sansaninsu da ke biranen Iskenderun da DiyarBakir suna dosar kan iyakar kasar da Syria.

An kuma ga tankunan yaki, da bingigogin kakkabo jiragen sama da kuma na harba makami mai linzami sun nufi garin Yayladagi dake kudancin Turkiyyar.

Haka ma kamfanin dillancin labaran kasar, Anatolia, ya ce ana jigilar motoci masu sulke zuwa wadansu sassan kan iyakar a garin Sanliurfa; yayinda aka jibge wadansu daga cikin makaman a garin na Yayladagi kusa da inda aka harbo jirgin kasar ta Turkiyya a makon jiya.

Gwamnatin Turkiyya dai ta riga ta sanar da sababbin ka’idojin da karya su zai sanya sojan nata su kai hari.

A cewarta, duk wani sojan Syria da ya kusanto iyakarta za a dauke shi a matsayin mai mugun nufi kuma za a iya kai masa hari.

Gwamnatin kasar ta Turkiyya dai ta ce jiragen yakin Syria sun yi ta keta hurumin sararin samaniyarta fiye da sau dari a bana amma ba tare da ta dauki wani mataki ba, amma yanzu tun da kidan ya sauya rawar ma za ta iya sauyawa.

Wannan matakin dai ya zo ne kasa da mako daya bayan sojan Syria sun harbo wani jirgin yakin Turkiyya a Tekun Mediterranean.

Tura makaman da kuma sojojin da Turkiyya ta yi dai ya zo gabanin shugaban kasar, Abdallah Gul, ya shugabanci wani taron majalisar tsaro ta kasa da aka yi ranar Alhamis.

Ana jin taron, wanda ministoci da kuma manyan hafsoshin soji suka halarta, ya mayar da hankali ne a kan zaman tankiyar da ke hauhawa tsakanin kasar da Syria.

A ranar Laraba ministan yada labaran kasar ta Syria ya shaidawa wani gidan talabijin na Turkiyya mai suna Ahbaar cewa mai yiwuwa ne sojojin kasar sun dauka jirgin na Turkiyya da suka harbo na kasar Isra’ila ne, yana mai karawa da cewa kasarsa ba ta neman fada da Turkiyya.

Ministan, Umran Al Zubaidi, ya ce jiragen yakin Turkiyya da na Isra'ila yawanci kirar Amurka ne; watakila shi ne ya sanya sojojin na Syria suka yi kuskure suka dauka jirgin yakin Isra'ila ne.

Hukumomin Turkiyya dai sun ce har ya zuwa yanzu ana ci gaba da laluben matukan jirgin su biyu, amma dai an debe tsammanin samunsu da rai.