An yi zanga-zangar dimokuradiyya a Hong Kong

Masu zanga-zanga a Hong Kong Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Dubban mutane sun shiga zanga-zangar dimokuradiyya a Hong Kong

Dubban mutane sun shiga wata zanga-zangar neman mulkin dimokuradiyya a Hong Kong, bayan nada sabon jagora ga yankin—wanda Burtaniya ta yiwa mulkin mallaka—a daidai lokacin da ake bikin cika shekaru goma sha biyar da mayar da yankin hannun China.

Sabon jagoran, C.Y. Leung, ya yi alkawarin kare hakkokin al'umma; sai dai kuma masu zanga-zangar sun bukaci kammalallen tsarin dimokuradiyya da kuma kawar da bambance-bambance a tsakanin al'aumma.

Masu zanga-zangar sun yi ta rera wakoki suna cewa “Leung Chun-ying, ka kare 'yanci da dimokuradiyya, ka yi murabus”.

Daya daga cikin masu zanga-zangar ya ce sannu a hankali Jam'iyyar Kwaminis ta China za ta kai Hong Kong ta baro.

Tun da farko dai Shugaba Hu Jintao na China ya ce Hong Kong ta bayar da gagarumar gudummawa ga yunkurin China na aiwatar da sauye-sauye.