Mahaukaciyar guguwa a Amurka ta halaka mutane 12

Mahaukaciyar guguwa Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Mahaukaciyar guguwa

Ruwan sama da tsawa tare da iska mai karfin gaske da aka yi a gabashin Amurka ya hallaka a kalla mutane 12.

Mutane kimanin million biyu ne a jihohin Amurka guda 9 ke zaune cikin rashin makamashin lantarki, sakamakon iska mai karfi daga mahaukaciyar guguwa, wadda ta taso daga tsakiyar yammacin babban birnin kasar Washington DC.

Mahaukaciyar guguwar na zuwa ne bayan wani zafi mai tsanani wanda ya shafi kusan kashi ukku cikin goma na kasar.

A birnin Washington, yanayin zafin ya kai makin digrin celcius 40, wanda bai taba ganin irin wannan zafi a cikin watan Yuni ba, tun wanda aka yi a shekarar 1934.

Karin bayani